20/06/2026
💻🤖 MENENE PROMPT ENGINEERING?
A wannan zamanin na AI, ana yawan jin kalmar Prompt Engineering.
Prompt Engineering na nufin: 👉 yadda ake rubuta umarni ko tambayoyi ga AI domin a samu amsa mai kyau da inganci.
AI k**ar ChatGPT tana dogara ne da abin da ka rubuta.
Idan tambayarka ba ta bayyana ba, amsar ma za ta iya zama ba daidai yadda kake so ba.
Misali:
❌ "Rubuta min game da AI."
✅ "Rubuta min bayani kan AI a Hausa cikin layi 15 tare da misalai 5."
Za ka ga cewa umarni na biyu ya fi bayyana abin da ake bukata.
Prompt Engineering yana taimakawa wajen:
• Rubuta articles da posts.
• Samar da ideas.
• Koyon programming.
• Kirkirar hotuna da AI.
• Bincike da nazarin bayanai.
A yau, kamfanoni da dama suna neman mutanen da s**a fahimci yadda ake amfani da AI yadda ya k**ata.
Saboda haka, koyon Prompt Engineering na iya zama daya daga cikin muhimman skills na wannan zamani.
Ka tuna: 👉 Ingancin amsar AI yana farawa ne daga ingancin tambayar da ka yi.