Abubakar Isah

Abubakar Isah Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Abubakar Isah, Information Technology Company, Bauchi, Azare.

"Dama ai falle ɗaya ce a jam'iyyar NNPP, kuma za mu yi falle na biyu a APC, ita kuma jam'iyyar ADC da su ka koma, ko fal...
06/04/2026

"Dama ai falle ɗaya ce a jam'iyyar NNPP, kuma za mu yi falle na biyu a APC, ita kuma jam'iyyar ADC da su ka koma, ko falle ɗaya ba za ta yi ba har abada" - Gwamna Abba.

YANZU-YANZU: Allah ne ke bayar da mulki, amma Kwankwaso shi ne ɗan siyasar da ke da tasiri wajen yanke hukuncin wanda ke...
05/04/2026

YANZU-YANZU: Allah ne ke bayar da mulki, amma Kwankwaso shi ne ɗan siyasar da ke da tasiri wajen yanke hukuncin wanda ke lashe zaɓen shugaban ƙasa a Nijeriya. Saboda Kwankwaso ne na sha kaye a zaɓen 2015, in ji Goodluck Jonathan.

Tsohon shugaban ƙasar Nijeriya, Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa Bola Ahmed Tinubu na iya fāɗuwa a zaɓe idan Rabiu Musa Kwankwaso ya koma gefen Atiku Abubakar. Ya ce yawan gwamnoni ba lallai ba ne ya hana ɗan takara shan kaye a lokacin zaɓe.

Goodluck Jonathan ya ce:
“A zaɓen shekarar 2015, ina da gwamnoni 28 a bayana, tare da mataimakin shugaban ƙasa daga Arewa maso Yamma. Duk da wannan fa’ida ta siyasa, sak**akon zaɓen ya nuna akasin haka, domin Kwankwaso ba ya tare da ni, kuma hakan ya sa na sha kaye a hannun Muhammadu Buhari.”

Ya ƙara da cewa:
“A yau ma, ina ganin wani yanayi mai k**a da wannan. Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na da gwamnoni 30 da ke mara masa baya, tare da mataimakin shugaban ƙasa daga Arewa maso Gabas. Sai dai ina ganin idan Kwankwaso bai shiga jam’iyyar APC ba, hakan na iya shafar nasarar Tinubu a zaɓen 2027.”

Ku yi following Jaridar ATV Hausa.

An k**a wani matashi da ya sanya kayan soja na bogi a Angwan Rukuba, Jihar Plateau,sunansa Ezekiel Joseph ne, ba Yohana ...
05/04/2026

An k**a wani matashi da ya sanya kayan soja na bogi a Angwan Rukuba, Jihar Plateau,
sunansa Ezekiel Joseph ne, ba Yohana Audu ba k**ar yadda wasu rahotanni ke yadawa.

Jami’an ‘yan sanda ne s**a cafke shi yayin da yake sanye da kayan sojoji, kuma aka same shi dauke da katin shaidar makarantar sojin Najeriya (Nigerian Military School) na bogi.

Wannan kamen yana da alaka da harin ranar Palm Sunday da aka kai a unguwar Angwan Rukuba, inda sama da mutane 30 s**a rasa rayukansu.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Plateau ta tabbatar da k**a Ezekiel Joseph tare da wasu mutane shida da ake zargi da hannu a harin. A halin yanzu, jami’an tsaro na gudanar da cikakken bincike domin gano dukkanin wadanda ke da hannu a wannan hari da kuma rushe cibiyar da ke bayansa.

Da Addini Ake Shirya Jana’izarmu!Akwai wani mataki da in jahilcinka ya kai to hakan yana zama babban makami ne a hannun ...
05/04/2026

Da Addini Ake Shirya Jana’izarmu!

Akwai wani mataki da in jahilcinka ya kai to hakan yana zama babban makami ne a hannun makiyanka.

Abin da yake faruwa a Najeriya a halin yanzu, musamman abubuwan da s**a shafi rikicin Jos da sauran sassan kasar nan, ba yaki ne na neman gaskiya ko bayyana ta ba; Surgical Operation ne da aka kera don raba zuciyar talaka musulmi da talaka kirista.

Kafin bayyanar wadannan mutane biyu da kuke gani, musamman wannan bako mai suna Alex, al’ummar kasar nan suna da wani tsari na Tolerance (hakuri da juna). Sun san cewa duk wanda zai biyo dare ya kashe mutane, bazai tambayeka addini ba kafin ya harba harsashi.

Amma yau, an shigo da gubar da take nuna wa kowane bangare cewa shi kadai ake nema a kashe, musamman kiristoci sunfi Shan wannan gubar duk da sanin gubar zatayi musu illa anan gaba.

Wannan bawan Allah mai suna Alex yana tafiya ne da ajandar da muke kira Divide and Rule (Raba ka mulka). Yana rura wutar cewa wai kiristoci ne kawai ake hara, alhalin gaskiyar magana ita ce, harsashin bindiga baya zabar fata ko aqida; musulmi ma kashe su ake yi, kiristoci ma ana kashe su.

Abin bakin ciki shi ne, idan wannan wutar ta Religious War tafi karfin kiristocin, Alex fa ba zai tsaya ya gani ba, Kuma bazai tsaya ya karesu ba. Yana da Dual Citizenship, yana da International Passport. Da zarar jini ya fara malala a titunan Jos ko Kaduna, zai dauki kayansa ya koma kasashen waje ya bar ni da kai muna karar da kanmu, k**ar yadda na samu Labarin harya gudu ya barmu.

Yakin addini ba k**ar harin ‘yan ta’adda ba ne; ‘yan ta’adda suna bugawa ne su gudu, amma yakin addini ciwo ne da yake zama a gida, yana tashi da safe, ya kwanta daddare, kuma babu gwamnatin da ta isa ta tsayar da shi muddin zuciya ta riga ta baci.

Ya k**ata mu tambayi kanmu: Wane ne yake cin ribar wannan?

Ilimin Physics ya koya mana cewa duk inda aka samu Friction (gogayya), to ana samun Heat (zafi). Wannan zafin da suke samarwa a tsakaninmu shi ne yake ba su damar cigaba da satar😡

Kaɗan daga cikin Yarjejeniya Tsakanin Kwankwaso da jam'iyar ADCWasu rahotanni sun bayyana cewa an cimma wata yarjejeniya...
05/04/2026

Kaɗan daga cikin Yarjejeniya Tsakanin Kwankwaso da jam'iyar ADC

Wasu rahotanni sun bayyana cewa an cimma wata yarjejeniya tsakanin Rabiu Musa Kwankwaso da manyan shugabannin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a matakin ƙasa.

Bisa ga bayanan da ke yawo, an amince cewa Kwankwaso ne zai bayar da ɗan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar, tare da kasancewarsa jagoran ADC a jihar. Haka kuma, ana zargin cewa shi ne zai ba da sunan wanda zai zama shugaban jam’iyyar a Kano.

Rahotannin sun kuma nuna cewa za a ba shi wata muhimmiyar kujera a shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa idan aka gudanar da babban taron jam’iyyar (convention).

Dangane da zaɓen shugaban ƙasa, an ce Kwankwaso zai shiga zaɓen fidda gwani, inda aka cimma cewa duk wanda ya yi nasara, sauran za su mara masa baya domin haɗin kai.

Sai dai har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga jam’iyyar ADC da ke tabbatar da wannan yarjejeniya.

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta sanar da naɗa wakilai a birane 12 na ƙasashen waje, a wani yunkuri na jaw...
05/04/2026

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta sanar da naɗa wakilai a birane 12 na ƙasashen waje, a wani yunkuri na jawo hankalin al’ummar duniya kan abin da ta bayyana a matsayin ƙara tabarbarewar dimokuraɗiyya da kuma matsin lamba da ake yi wa ‘yan adawa a Najeriya.

Jam’iyyar ta ce manufar wannan mataki ita ce ƙarfafa hulɗa da gwamnatocin ƙasashen waje, tare da isar da saƙonta kai tsaye domin kauce wa abin da ta kira yaɗa ra’ayi mai bangare guda daga ɓangaren gwamnatin tarayya game da halin da ake ciki a ƙasar.

Wannan mataki na ADC ya zo ne bayan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, wato INEC, ta soke amincewa da shugabancin jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin David Mark, tare da kuma ɓangaren jam’iyyar da Nafiu Bala ke jagoranta, a ranar Laraba da ta gabata.

ADC ta bayyana cewa wannan lamari na daga cikin dalilan da s**a sa ta ɗauki wannan sabon mataki, domin neman fahimta da goyon baya daga ƙasashen duniya, tare da bayyana matsayinta kan abin da ke faruwa a harkokin siyasar Najeriya.

Ko wannan mataki da ADC ta ɗauka zai iya tasiri a yadda ƙasashen duniya ke kallon dimokuraɗiyyar Najeriya?

Duk wanda aka zaga, yana iya mayar da martani dai-dai da abin da aka yi masa. Sai dai wajibi ne a sani: taba mutuncin AN...
04/04/2026

Duk wanda aka zaga, yana iya mayar da martani dai-dai da abin da aka yi masa. Sai dai wajibi ne a sani: taba mutuncin ANNABI (S.A.W) jan layi ne da ba a ketarawa, domin darajarsa ta fi karfin wasa ko wulakanci.

Idan kuma mutum ya ketare iyaka, to za mu hukunta ka da ayoyin Allah, k**ar yadda ake hukunta shedanun aljanu.

Mu zauna lafiya, mu girmama juna. Amma kowa ya sani, akwai layin da ba a tabawa shi ne mutuncin fiyayyen halitta ANNABI MUHAMMADU (S.A.W).

Sako Daga Dan Wasan Hausa BMB

Jiya na gama magana cewar Gwamnan Jihar Bauchi Sen Bala shine Gwamnan da nikeso ya shigo mana ADC, saboda rikicin jam'iy...
04/04/2026

Jiya na gama magana cewar Gwamnan Jihar Bauchi Sen Bala shine Gwamnan da nikeso ya shigo mana ADC, saboda rikicin jam'iyyar PDP ta su.

Alhamdulillahi, yau da kansa ya bayyana akwai yiwuwar ya shiga ADC, saboda abinda ke faruwa a cikin PDP, kuma ya nuna ba zasu shiga jam'iyyar da ba'a son su ba, wato APC.

Idan Gwamna Bala ya shigo, tabbas wata ƙwarin gwuiwa ne musamman a Arewa masoya gabas. Yana da ƙwarewa, gogewa, da rashin tsoro. Kuma ko ba komai Bauchi sun samu Shugabanci mai inganci a gunsa.

Allah Ubangiji ya bada ikon shigowa ADC Gwamna.

Hoton da aka saka, kawai an yi amfani dashi ne don ya ƙarawa rubutun armashi✌️

Address

Bauchi
Azare
751101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abubakar Isah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share