Dandalin Fasahar Android

Dandalin Fasahar Android Hbd

26/07/2025

Bari muyi misali a wannan number wayar +23408137350232, numbers guda 11 ne idan kuma aka hada da +234 ya k**a guda 14 shin me ko wacce lambar take nufi?

✅Wadannan numbers din na farko guda ukku: "+234" itace lambar dake nuna ƙasar da number wayar take, ma'ana duk inda kaga lambar waya ta fara da "+234" to number Nigeria ce, kuma nigeria kadai ce ke amfani da wadannan lambobin.

Kowace ƙasa tana da nata lambar, Misali:

🇳🇬 Nigeria: +234
🇺🇸 America: +1
🇬🇧 UK (Birtaniya): +44

Don haka "+234" na nuna cewa wannan lamba tana kasar Nigeria.

✅Lambobi guda ukku dake gaban "+234" wato wadannan kenan: "813" su ana kiran su da suna Prefix, wadannan numbers guda ukku dasu ne zaka iya gane wane kalan layi ne kake amfani dashi, ma'ana wanne kamfanin sadarwa ne kake amfani dashi, domin ko wanne kamfanin sadarwa suna da nasu lambobin guda ukku.

Ga wasu misalai:

--0803`, '0813', '0703' wannan duka layin MTN ne.

--'0802', '0812' wannan duka layin Airtel ne.

--'0805', '0815' wannan duka layin Glo ne.

--'0809', '0817' wannan duka layin 9mobile (Etisalat) ne.

Idan kuka duba number wayar da na saka a farko tana da '813', wato kenan layin MTN ne.

✅Sai kuma sauran lambobi guda bakwai dake karshe, wato wadannan "7350232" ana kiran su da suna subscriber number.

Wannan 7-digit din da yake zuwa a ƙarshe a ko wanne layi, keɓantaccen lambobi ne gare ka kai kaɗai, ba wanda zai iya samun irinsu a ko wane layin MTN, GLO, Airtel ko 9Mobile sai kai.

Ga wasu jerin Lambobin Prefix da sunan kamfanonin sadarwar da suke da su ta yadda duk sanda kaga layin MTN, Airtel ko Glo zaka gane ko layin menene.

(0803, 0806, 0703, 0813, 0816, 0903, 0913, 0706 duka layin MTN ne.)

(0802, 0808, 0708, 0812, 0701, 0901, 0902, 0907, 0912 duka layin Airtel ne)

(0805, 0807, 0705, 0815, 0811, 0905, 0915 duka layin Glo ne)

(0809, 0817, 0818, 0909, 0908 duka layin 9mobile ne (tsohon layin Etisalat)).

21/06/2025

Barkannu da dare

Address

Tafawa-Balewa
Bauchi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dandalin Fasahar Android posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Dandalin Fasahar Android:

Share