Mayerk digital world

Mayerk digital world I am Idris d Ahmad CEO founder mayerk digital world
Ethical hacker/cyber security/researcher/ blogger

Wannan CODE din da kuke gani yana da Abubuwa da yawa. Ga wasu daga ciki kamar haka1) Mayar da wayar ka 5G Network2) Amfa...
26/10/2023

Wannan CODE din da kuke gani yana da Abubuwa da yawa. Ga wasu daga ciki kamar haka

1) Mayar da wayar ka 5G Network
2) Amfani da Datar wayar ka koda tana Airplane mode
3) Qarawa wayar ka sauri
4) Tracking din network din wayar ka
5) Zakaga duk abinda matar ka ko budurwar ka takeyi a wayar ta.
Da dai sauran su.

Ina cikin bincike na yau naci karo da wata apk Wanda zata taimaka sosai wajen da kuma dakile matsalar satar waya a tsaka...
04/08/2023

Ina cikin bincike na yau naci karo da wata apk Wanda zata taimaka sosai wajen da kuma dakile matsalar satar waya a tsakanin mutane!!!

Ga kadan daga cikin aikin wannan app din

1.tana bada sanarwa a duk lkcn da Wani ya motsa maka waya (phone) misali idon wayar ka tana aljihun ka sai Wani yasaka hannun sa ya tabata to Nan take zatayi Kara (Ring) ta baka sanarwa Nan take.

2.sanan tana magance matsalar masu cire maka waya a chaji wasu mutanan dazaran ka Saka wayar ka chaji zasu zo su cire maka ko kuma su sace maka wayar,
To wanan manhajar zata taimaka maka wajen baka sanarwa Nan take.

3.tana maganin masu kutse wato (intruder) ta hanyar baka sanarwa Nan take
4. Sannan tana bada taimako wajen kusancin hannu ta yadda da zaran mutum yayi yunkurin taba wayar ka zata sanar dakai Nan take.
Ga link wnn app din akasa 👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.antitheftalarm.donttouchmyphone.phonesecurity

Allah ya https://play.google.com/store/apps/details?id=com.antitheftalarm.donttouchmyphone.phonesecurity sa'a yakuma tsaremana wayoyin mu ameeen

Idris d Ahmad
CEOMMayerk digital worlddMayerk digital worldwMayerk digital world

Kasuwar yan damfara (scammers) ta fara buɗewa a yan kwanakin nan saboda zuwan Network din 5G a Nigeria.Post by Abubakar ...
05/07/2023

Kasuwar yan damfara (scammers) ta fara buɗewa a yan kwanakin nan saboda zuwan Network din 5G a Nigeria.

Post by Abubakar Sani Dan Bahaushe

Da yawan yan damfara (scammers) suna nan sun baza komar su domin damfarar duk wanda ya fada farkon su.

A hasashe mafi inganci, yan damfarar zasu kira ku ne ko kuma suyi maku sakon message akan cewa zasuyi maku upgrading na Network din ku daga 3G/4G zuwa 5G domin kara maku saurin Network a wayoyin Ku. Bugu da kari, suna iya cewa zasu baku kyautar data bayan sunyi maku upgrading din.

Daga lokacin da kuka amince akan suyi maku upgrading, to zasu turo naku da One Time Password (OTP) ko kuma kuma lambobin Token a cikin layin ku, sannan kuma su bukaci cewa ku tura masu domin kammala aikin upgrading din.

Wannan OPT din, yina iya yiwuwa daga bankin ka, social media handle ko kuma wani abu naka mai matukar amfani dake yanar gizo. Daga lokacin daga basu wadannan lambobin na OTP, to suna iya sace maka kudi a account na banki ya hanyar payment gateways, ko suyi maka hacking na social media handles ko kuma suyi maka kutse a wani abun naka mai amfani dake yanar gizo. Wanda hakan na iya jawo maka matsala da dama.

A yanzu haka an fara yin cyber kidnapping. Bana so nayi magana sosai a wannan wajen saboda tsaro da kulawa. Amma dai, kada ka yarda wani yace ka kashe wayar ka na tsawon lokaci saboda zai maka upgrading zuwa 5G.

Kamfanonin layin da kuke amfani dashi ne kadai suke da hurumin yin maku upgrading. Dan haka mai bukatar ayi masa upgrading sai ya ziyarci ofishin kamfanin layin da yake amfani dashi ko kuma ya ziyarci jami'in su mafi kusa.

Duk wayar da aka shiryata domin amsar network din 4G kadai, to babu yadda za'ayi ta koma 5G koda kuwa anyi upgrading din layin dake a cikin wayar zuwa 5G. Mai bukatar amfani da Network din 5G, sai ya siya wayar da aka kirkireta domin tayi amfani da 5G

A kula sannan kuma a kiyaye da yan damfara.

Idris D Ahmad
CEOMayerk digital world

A KULA SOSAIAbu ɗaya da yakamata kasani cewa masu ƙwacen waya sunfi damuwa da sim card dinka fa, akwai wasu dake gefe wa...
11/06/2023

A KULA SOSAI

Abu ɗaya da yakamata kasani cewa masu ƙwacen waya sunfi damuwa da sim card dinka fa, akwai wasu dake gefe wadanda da zarar an saci wayarka to su sim card din suke buqata SBD su kwashe maka dukiyarka dake bankinka, SBD ansan dai duk taqamarka shine ace kana da kudi a banki.

Kana ankarewa an sace maka waya to kada ka tsaya tunanin wani kiran bankinka ko zuwa banki cikin gaggawa, domin idan kiransu zakayi kafin su ɗaga kuyi magana tunin anyi maka abinda za'ayi.

Haka ma idan zuwa zakayi nan ma kafin kaje ka shiga cikin bankin anyi abinda za'ayi.

Hanya mafi sauqi shine ka ari wayar wani dake kusa dakai domin toshe bankinka ta yadda kuɗi ba zai fita ba sai dai ya shiga, ina nufin da kanka zaka iya kulle account dinka ta yadda kuɗi ba zai fita ba sai dai ya shiga.

Kusan kowanne banki akwai hanyoyin toshewar kada kuɗi ya fita, ga jerin bankunan da hanyar toshewar:

1.Access Bank: * 901 * 911 #
2. Zenith Bank: * 966 * 911 #
3. GTB Bank: * 737 * 51 * 74 #
4. WEMA Bank: * 945 * 911 #
5. First Bank: * 894 * 911 #
6. Key Stone Bank: * 7111 * 911 #
7. UBA Bank: * 919 * 911 #
8. FCMB Bank: * 329 * 911 #
9. Sterling Bank: * 822 * 911 #
10. Unity Bank: * 7799 * 911 #
11. Fidelity Bank: * 770 * 911 #
12. Heritage Bank: * 745 * 7 #
I3. Ecobank * 326 * 911 #
14. Union Bank * 826 * 911 #
15. Stanbic Bank * 909 * 911 #
16. Polaris Bank * 833 * 911 #

Zaka iyayi a kowanne layi ba lallai sai layinka ba, kawai bayan kasaka account number zasu buƙaci kasaka lambar da kakejin alert na wannan account din, shikenan zasu kulle kuɗi ba zai iya fita ba, duk randa kayi swap kuma to dole sai kaje bankinka sune zasu iya budewa komai yadawo yadda yake.

Allah ya tsaremu, a guji saka waya a aljihun gefe na riga ko aljihun gaban riga. Ka tabbatar wayarka tana inda ana kai hannu zakaji.
Idris d Ahmad ✍️
CEOMayerk digital world

Dan Allah kuyi sharing Dan Wasu Su anfana

Nan na kawo muku maganar samun 10k a palmpay kuka karya ta Ni.Wallahi tallahi yanzun nan aka sake turomin wata.Har yanzu...
03/06/2023

Nan na kawo muku maganar samun 10k a palmpay kuka karya ta Ni.
Wallahi tallahi yanzun nan aka sake turomin wata.
Har yanzu indai kana da.
Layin da ba'a bude palmpay da shi ba
In Sha Allah Zan guiding yanda zaka samu. 10k Kawai Kayi Mgn Idan Kana Da Layi Da Ba'ataba Bude Palmpay Dashiba
Just DM

Sabbin Tsarukan MTN Sun Fara Aiki  Kuma An Dakatar Da Duka Tsoffin.Ga Yadda Sabbin Code Ɗinsu Yake:Idan Zaka Sa Airtime ...
17/05/2023

Sabbin Tsarukan MTN Sun Fara Aiki Kuma An Dakatar Da Duka Tsoffin.

Ga Yadda Sabbin Code Ɗinsu Yake:

Idan Zaka Sa Airtime (Kati) *311*Pin # Maimakon *555*Pin #.

Idan Zaka Checking Balance (Duba Asusun Ka): *310 # Maimakon *556 #

Idan Zaka Ciyo Rancen Kuɗi:
*303 # Maimakon *606 #

Idan Zaka Sayi Data'r Kamfani:
*312 # Maimakon *131 #
Idris d Ahmad ✍️
CEOMayerk digital world

Assalamualaikum, Masu amfani da MTN ga wata code wanda zaku samu 1.5gb a ₦150 sannan 4gb a ₦500 kacal.... Read more
06/05/2023

Assalamualaikum, Masu amfani da MTN ga wata code wanda zaku samu 1.5gb a ₦150 sannan 4gb a ₦500 kacal.... Read more

INATA KOKARIN YI MAKA TRANSFER AMMA NETWORK YA HANA!🤦🏽‍♂️Ana yiwa network sharri da yawa faaah (wani lokacin ba matsalar...
10/03/2023

INATA KOKARIN YI MAKA TRANSFER AMMA NETWORK YA HANA!🤦🏽‍♂️

Ana yiwa network sharri da yawa faaah (wani lokacin ba matsalar "NETWORK" bane na "INTERNET" ne).

NETWORK 🆚 INTERNET

A duk lokacin da kake shirin tura sako ko kuma kudi ta hanyar amfani da mobile data, sannan kasamu matsala sakonnan bai jeba, toh matsalar ka iya bayuwa ga "NETWORK🖇️" ko kuma "INTERNET🌐".

Tayaya zaka gane matsalar daga "NETWORK" ne?
Mu dauki "WhatsApp" a misali:
Mu dauka ka tura sako ta _WhatsApp_ sai kaga sakon nan bai tafi ba, kar kayi saurin yanke hukunci na cewa matsalar network/internet ne, a'a sai kayi kokari ka tsallaka _Telegram_, shima ka gwada tura sako ka gani ko zaije, in har sakon still baije ba a telegram, Toh matsalar ka daga "NETWORK" ne (Anan zata iya yiyuwa inda kake ba service ko kuma kamfanin layin da kake amfani dashi ne s**a samu tangarda e.g MTN, Airtel e.t.c)🔅

Tayaya zaka gane matsalar daga "INTERNET" ne?
Still dai mu dauki WhatsApp da Telegram a misalin:
Idan har ka tura sako a WhatsApp bai jeba sannan ka gwada a telegram yaje, Toh hakan yana nufin matsalar daga Internet ne (Server din WhatsApp baiyi connecting da network din wayar ka ba)
*Anan wajen babu ruwan network, ma'ana babu ruwan kamfanin layin da kake amfani dashi e.g MTN, Airtel e.t.c*🔆

PS: Connection din dake tsakanin "NETWORK" din wayar ka da _Server_ shi ne "INTERNET" (kafin ka hau social media kamar facebook, sai network din wayar ka yayi connecting da Server din kamfanin facebook wato Meta).📶

Ga wata yar tambaya: Lokacin da Facebook, WhatsApp da Instagram s**a dauke, matsalar daga ina ne NETWORK Koh INTERNET?

• Idris d Ahmad CEOMayerk dMayerk digital world worldMayerk digital world

Ga wani Bonus da naga ana bayar dashi ga masu amfani da Airtel, zaka danna *234 # zai bayyanar maka da Options sai ka da...
19/10/2022

Ga wani Bonus da naga ana bayar dashi ga masu amfani da Airtel, zaka danna *234 # zai bayyanar maka da Options sai ka danna na farko da aka rubuta "Talkmore" kana dannawa zai baka Options, ka zabi irin Bonus din da kakeso, akwai wanda zaka saka 100 ka samu Bonus din 500, akwai wanda zaka saka 200 ka samu Bonus din 1000 haka zalika 300 kasamu 1500 haka dai kudin zasu dinga nunkawa har idan ka saka 1000 kasamu 5000.

Wannan tsarin zai taimaki samari da yammata masu soyayya..😁

Allah Yataimaka..🙏

Address

Gombe

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mayerk digital world posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share