16/09/2025
Gyaran suna ko shekarun haihuwa a BVN yana da matakai na musamman da dole ne a bi su cikin tsari. Ga yadda ake yin sa.
Abubuwa Masu Muhimmanci da Ya Kamata Ka Lura dasu.
Akwai BVN ta Banki, akwai ta Café duk ga Bayanin yadda zakuyi a kasa 👇
1. Duk bayanan ka a BVN dole su yi daidai da na ID card É—inka da sauran takardun ka.
2. Ka tabbatar da cewa takardun ka suna da sahihanci kuma an amince da su daga hukumomi.
3. Idan sunanka ko shekarunka sun bambanta da na bankuna da dama, dole ka gyara su É—aya bayan É—aya.
Na farko, idan a Banki kayi BVN dinka
Kaje Zuwa Bankin Da Aka Yi Rijistar BVN É—inka ma'ana duk branch din kake kusa dasu
Sannan Ka tambayi fom na BVN Data Correction Form. Ka coke duk bayanan da s**a bukata a form din. Amma ya zama wajibi ka gabatar da musu da 👇
1. Means of ID k**a National ID card dake dauke da suna daidai da abinda kake son chanzawa.
2. Affidavit daga kotu
Wannan sune hanyoyi mafi sauki wajen gyaran BVN dinka a Banki.
Abu na Biyu, idan a Café ko Business Center kayi.
Ka ziyarci Wanda yayi maka ko wani Cafe din mafi kusa Ka sanarda su bukatarka. Bayan kaje kotu kayi affidavit.
Ga waÉ—anda s**ayi a Cafe amma Basu fahimci yadda zasuyi ba. Zaku iya shiga wannan shudin rubutun https://wa.me/message/YJOWYVSK7KTBF1 ko Ku yiwa wannan Lambar 08108029064 magana ta WhatsApp don ganawa da mu kai tsaye.
FilePro... Domin saukaka muku.