19/04/2026
ƘWARON NAIRA MILIYAN 122
STAG BEETLE – ƘWARON DA YA FI KOWANE TSADA A DUNIYA
Stag beetle wani irin ƙwaro ne da ya shahara sosai saboda manyan “ƙahon” bakinsa masu k**a da na barewa. Wannan ne ya sa ake kiransa stag beetle. Yana rayuwa ne a cikin tsoffin itatuwa masu rubewa, kuma maza s**an yi amfani da ƙahon bakinsu wajen faɗa domin neman mace.
Abin da ya sa ya fi sauran kwari tsada shi ne wahalar samunsa, girman jikinsa, tsawon ƙahonsa, da kuma sha’awar masu tarin kwari musamman a Japan da wasu ƙasashe na Asia. Wasu nau’ikan da aka saba samu farashinsu kan kasance ƙasa, amma nau’ikan da s**a yi wuya sosai suna kaiwa manyan kuɗaɗe.
Akwai wani rare species da aka taɓa sayarwa kusan dala 90,000. Idan aka juya da canjin kuɗin yau na kusan $1 = ₦1,359.55, wannan ya kai kusan:
₦122,359,500
Wato a taƙaice, stag beetle na musamman zai iya kaiwa kusan miliyan 122 naira.
Wannan ne ya sa ake ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin kwari mafi tsada a duniya, musamman idan ya kasance babba, rare, kuma yana da dogon ƙaho.