11/07/2026
📱 Meta Ta Cire AI Feature Da Ke Bawa Kowa Damar Yin Deepfake Da Hotonka — Ba Tare Da Izininka Ba!
Shin ka san cewa Meta ta taɓa gabatar da wani AI feature akan Instagram mai suna Muse Image, wanda ke bawa kowa damar @-mention wani public account (koda ba naka bane) sannan AI ta generate hotuna daga posts din, ba tare da an tambayi mai account din izini ba?
Meta ta ce manufar feature din shine domin taimaka wa mutane su design custom invitation ko su yi creative concepts. Amma bayan mutane da yawa s**a koka, har da kamfanin Hollywood na CAA (wanda ke wakiltar shahararrun mutane kamar Tom Hanks da Meryl Streep) da kuma union din SAG-AFTRA, Meta ta yanke shawarar cire feature din gaba daya, tana mai cewa feature din "bai yi daidai ba" (missed the mark).
💡 Darasi: Idan account naka public ne akan Instagram, koyaushe duba Settings dinka — musamman option din "Allow people to create with and reuse your content." Idan baka son wani ya yi amfani da hotonka wajen AI generation, ka toggle off wannan option ko ka mai da account dinka private.
Privacy dinka na hannunka ne — kar ka bari technology ta wuce ka!
Shin ka taɓa duba Settings na Instagram dinka domin ka ga ko wani zai iya yin amfani da hotonka ta hanyar AI? Bari mu ji ra'ayinka a comment! 👇