05/04/2026
Rikicin Siyasar Samun Yanci Kai A Kano 1953 Wanda Akafi Sani Da Turanci (Kano Riot)
Abin da ya jawo wannan tarzoma shi ne tabarbarewar dangantakar da ke tsakanin shugabannin siyasar Arewa da na Kudu a kan batun cin gashin kai a shekarar 1956. Wannan ya taso ne tun a shekarar 1953 da aka gabatar wa Majalisar Wakilai ta 1953.
Memba na Jama'iyar Action Group (AG), Cif Anthony Enahoro ya gabatar da kudiri a shekarar 1953 cewa: lokaci yayi da Najeriya zata samu ‘yancin kai a shekarar 1956. Shugabannin Arewa sun yi watsi da wannan kudiri. Lamarin ya ci tura wanda hakan ya haifar da rashin jituwa tsakanin shugabannin siyasar Arewa da na Kudu.
Kayar da kudirin ya harzuka jama’ar Legas, inda s**a mayar da martani Mai Zafi ga shugabannin siyasar Arewa inda s**a yi ta yi musu ihu da zagi a Legas, bayan dage zaman Majalisar a ranar 31 ga Maris, 1953.
Jam’iyyar (AG PARTY) ta ’yan kabilar Yarabawa ce zalla, (NCNC) ita kuma ta kabilar Igbo ce, kuma dukkansu sun amince da ’yancin kai a 1956, alhali kuwa ita Jam'iyar (NPC), wanda itace Jam'iyar Arewa tace bata amince ba. Sardauna jagoran Jam'iyar Yace: Arewa ba ta shirya a ba da mulki ba, dalilinsa shi ne, yan Arewa da yawa basu kammala karatun jami'a ba, su kuwa yan kudu tuni sunyi nisa a karatun boko, ba k**ar yan Arewa ba. Sardauna da sauran mayan Arewa sunji tsoron idan an bayar da mulki a 1956 yan kudu za su mamaye dukkan manyan muk**ai a Najeriya.
Wannan yasa Yan kudu su kai ta zagin Sardauna suna cewa ya hada baki da turawan mulkin mallaka don ka da a bai wa Najeriya yanci.
Da lokaci ya kure, AG da NCNC sun tura wasu mutane kano domin yin kamfen din goyon bayan neman yanci, hakan ya haifar da tashin hankali a Arewa lokacin da kungiyar Action Group ta ziyarci Kano a karshen mako na 15-17 ga Mayu, lamarin ya faru ne sak**akon kiyayyar da aka nunawa yan Arewa a Legas.
Da farko dai an gudanar da zanga-zangar cikin lumana wanda magoya bayan jam’iyyar Peoples Congress ta Arewa s**a gudanar
Amma washegari zanga-zangar ta rikide ta koma tarzoma.
Tashin hankalin ya fara ne a Otal din Turawan mulkin mallaka, a ranar 16 ga Mayu 1953 wanda a wurin za ayi taron jam'iyar Action Group karkashin jagorancin Akintola.
Kafin taron dai kungiyar ‘yan asalin Kano ta janye goyan bayanta da izinin da ta bayar nayin wannan taro. Daga bisani wasu gungun jama’a ne s**a taru a wajen otal din, inda s**a fara jifan mutanen da ke kusa da otal din, yayin da s**a tafka asara mai dinbin Yawa. Wasu mutane biyu da ake kyautata zaton ’yan Kudu ne sun mutu, daga bisani ’yan tarzomar sun yi yunkurin shiga Sabon Gari, amma jami’an ‘yan sandan kasar s**a fatattake su.
Lamarin ya kara ta’azzara kuma ya zama rikicin kabilanci a ranar 17 ga watan Mayu, lokacin da zauna Gari banza s**a fito daga yankin Arewacin Kano, musamman unguwar Fagge, wasu daga cikin masu tayar da tarzoma na dauke da bindigogi, s**a yi yunkurin kutsawa yankin Kudu da Ibo s**a mamaye yankin Sabon Gari, su kai sa'ar shiga, duk da cewa lamarin nasu na asali na kin Yarabawa ne, amma wadanda aka kashe a yankin Sabon Gari yawancinsu 'yan kabilar Igbo ne. Shaguna da suke ciki duk an wawashe su a Kasuwar Sabon Gari tare da kai munanan hare-hare.
An kira jami’an ‘yan sanda da na Sojoji tare da hana wasu barayin shiga yankin Sabon Garin. Rikicin ya ci gaba da barkewa a yankunan Kano musamman ma Fagge.
Bayan dokar hana fita a ranar 16 ga Mayu fadan ya lafa amma ya sake barkewa a washegari. A ranar 18 ga wata, an kai wani gagarumin dauki na 'yan sanda da sojoji zuwa Kano, an kuma kafa dokar ta-baci a duk fadin yankin. kuma an raba bangarorin da ke gaba da juna ta hanyar sa shingen waya.
Bayan Kura ta Lafa, an yi musayar fursunoni don a rage zaman dar-dar, an sako ’yan Kudu da aka k**a, su ma ’yan Arewa sun saki yan kudu, an bukaci ‘yan Arewa mazauna yankin Sabon Gari da su tashi, sannan aka bukaci ‘yan Kudu mazauna yankin Fagge da su koma Sabon Gari.
Kimanin ‘yan Najeriya 46 galibi ‘yan Arewa da kuma ‘yan kabilar Igbo ne s**a mutu a wannan arangamar, kuma an yi jinyar fiye da mutane 200 da s**a samu raunuka. Duk da cewa nan take gwamnatin mulkin mallaka a Najeriya ta kira abinda ya faru da rikicin kabilanci, amma shugabannin siyasa sun ce rikicin siyasa ne tsakanin mutanen da ke son mulkin kai a shekarar 1956 da kuma masu son ci gaba da mulkin mallaka.