Smartdata4u

Smartdata4u We offer instant recharge of Airtime, Databundle, CableTV (DStv, GOtv & Startimes), Electricity Bill Payment and more

01/09/2026

Allah ya Rahama Maka
Malam Ikara
Allah yasa Malami su karbi wannan Nasihar

31/08/2026
31/08/2026

Mutuna da Dalilin da Allah Ya halicci bayi (mutane),

Dalili kuwa shi ne su bauta Masa Shi kaɗai.
Allah ﷻ Ya ce:
وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ
“Ban halicci Aljannu da mutane ba face domin su bauta Mini.”
(Suratu adh-Dhāriyāt 51:56)
Ma’anar bautar Allah
Ba sallah kaɗai ba ce. Ta haɗa da:
Sallah da azumi
Yawaita zikiri da istigfari
Bin umarnin Allah da barin abin da Ya haramta
Kyautatawa iyaye da mutane
Yin duk wani aikin alheri da niyyar neman yardar Allah.
A takaice: An halicce mu ne domin mu san Allah, mu bauta Masa, mu bi Manzonsa ﷺ, sannan mu shirya domin komawa gare Shi.

30/08/2026

SALLAR DARE💚

Koda dare ya yi shiru, mutane suna barci, amma kai ka tashi ka tsaya a gaban Allah. dan uwa
Sallar dare ba wai raka'o'i ne kawai Akeyi ba; lokaci ne na kusanci da Allah, neman gafara, da roƙon buƙatunka👂.

Annabi ﷺ ya ce:
“Mafi falalar sallah bayan farillai ita ce sallar dare.”
Sahih Muslim
Ka tashi ko da raka'a biyu ne kacal, ka yi su da ikhlasi. Ka yi addu'a, ka nemi gafarar Allah, ka faɗi abin da ke cikin zuciyarka.

Wataƙila wannan dare ne Allah zai buɗe maka ƙofar da ka daɗe kana jira.
Kada ka ce “gobe zan fara.” Ka fara yau.

ALLAH BAKA IKO

18/04/2026

CIN ZARAFIN ADDINI DA TAUYE HAKKI NA DOKAR QASA!

Yanzu naga Labarin
Wata Daliba Musulma tazo zata shiga gurin da zasu rubuta jarabawa ta JAMB sai wata jami'ar tsaro na Civil Defence ta hanata shiga, ta koreta saboda hijabin ta

Amma ga wasu Dalibai sun zo tsirara an barsu sun shiga ba tare da wata tsangwama ba😢

Wannan cin zarafi da tauye hakkin addini da wulakanci ya faru ne a makarantar Peter Harvard School dake Kubwa a garin Abuja

Dokar Kasar Nigeria ya bawa kowa damar yin addininsa yadda ya ga dama ba tare da cutarwa, saka hijabi a gurin mace Musulma addini ne ba wai ganin dama ba

Abinda wannan jami'ar tsaro tayi fito na fito da dokar Kasa ne, wanda ya kamata a gudanar da kwakkwaran bincike domin ta fuskanci hukunci, domin zai iya haddasa fitina da tashin h@nkali

Kuma wannan yana kara bayyana mana cewa Musulmin Nigeria an gama cinye mu da yaki, ku yi tunanin in ba Musulma bace tazo zata shiga sai akace dole sai ta saka Hijabi? me kuke tunanin zai faru?

Yawan mu ya zama kamar bai da wani amfani, irin wannan wulakanci da cin fuska ya kamata ace ya jima da zama tsohon yayi🗣

Allah Yasa Mudace 🙌

Address

Dairah

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Smartdata4u posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Smartdata4u:

Share