26/09/2022
🔰AREWA REST-TECH CRYPTO🔰
BABI NA ƘARSHE AKAN KUƊI
SIFFOFIN DA YANAYIN KUƊI
Akwai siffofi da ɗabi'un nagarta da ya kamata duk wani abu da a ke amfani da shi a matsayin kuɗi ya kasance yana da su. Mafi yawan abubuwan da mutane s**a dinga amfani da su a matsayin kuɗi ba su gama cika ingantattu ba, saboda ba su gama haɗa dukkanin siffofin ba.
Kuɗi mai cikakken inganci shi ne wanda ya haɗa halayen nan guda shida:
1. Durable
2. Divisible
3. Transportable
4. Non-counterfeit able
5. Valuable
6. Generally accepted
1. Durable: Duk abin da za a yi amfani da shi a matsayin kuɗi ya kyautu abin ya kasance yana da; ƙarkon jimawa ta yadda za a iya adana shi na tsawon lokaci ba tare da ya lalace ba, komai tsawon lokacin da a ke amfani da shi ba zai koɗe ba, kalar jikinsa ba za ta canja ba, idan fari ne zai tabbata a matsayin farin ba zai koma wata kalar ba, idan an ajiye shi komai tsawon lokaci girman jikinsa da kaurinsa ba zai ragu ba, sannan yanayin zafi ko yanayin sanyi ba za su sanya ya ruɓe ko ya lalace ba. Bisa la'akari da haka za mu iya ganin da yawa daga cikin nau'ikan kuɗaɗen da al'umma daban-daban s**a yi amfani da su ba kowanne ne ya ke da ƙarkon da a ke buƙata ba, hatta kuɗaɗenmu na takardu ba su da ƙarkon jimawa sosai, saboda suna iya lalacewa ko su koɗe ko kuma su yayyage ya kasance sun yi lalacewar da ba za a karɓa ba sai dai a ƙona. Bai kamata kuma a ce kuɗaɗe za su iya lalacewa ta yadda mai su zai yi asara ba, kamata ya yi nagartarsu ta tabbata yadda mai su ba zai yi asara don ya ajiye su na tsawon lokaci ba. Amma zinare a matsayin kuɗi idan muka duba za mu ga yana da ƙarkon
da a ke buƙata; kalarsa ba ta koɗewa, adadinsa ba ya raguwa, ba ya lalacewa ballantana wanda ke da shi ya zam ya yi asara, komai tsawon
shekaru idan ka ajiye shi za ka same shi yana nan yadda ka ajiye shi.
Haka su ma kuɗaɗen digital kasancewar su lambobi to su ma ba sa lalacewa kuma ba sa koɗewa ko raguwa. Sai dai su kuɗaɗen digital da ya ke su nau'in kuɗin fiat ne da Gwamnati ke samarwa, ƙarkonsu ya ta'allaƙa ne da Gwamnati domin duk da ba sa lalacewa amma idan Gwamnati ta ce a daina karɓar su to sun tashi a matsayin kuɗi sun zama lambobin da ba su da bambanci da lambobin cikin calculator.
2. Divisible: Hali na biyu da ya kamata kuɗaɗe su kasance suna da su: su zama masu sauƙin rarrabawa ta yadda za a iya amfani da su a sayi manyan kayayyaki da ƙananun kayayyaki. Amma idan ya kasance ba za a iya amfani da su a sayi ƙananun abubuwa ba sai dai manya, to ba su gama cika siffofin da za a iya kiransu da kuɗaɗe ingantattu ba. A wannan fannin idan muka duba za mu ga abubuwa da yawa da aka yi amfani da su a matsayin kuɗi kamar; gishiri, sulallan zinare, kuɗaɗen takarda dama kuɗaɗen lambobi, dukkaninsu ana iya amfani da su a sayi manyan kayayyaki har ma da ƙananu.
3. Transportable: Kafin kuɗaɗe su gama cika ingantattu, dole sai idan ana iya ɗaukar su a
yi tafiya da su daga wani guri zuwa wani guri ba tare da an sha wahala sosai ba. Amma idan ya kasance kuɗaɗe ba za ka iya ɗaukar su ta daɗi ka tafi da su kasuwa ka yi sayayya ba, to suna da rauni ta fuskar inganci.
A wannan ma idan muka duba za mu ga abubuwa da yawa da aka yi amfani da su a matsayin kuɗi yawancin su ana iya ɗaukar su ayi zirgazirga da su ta daɗi, sai dai wasu sun fi wasu sauƙin zirga zirga-zirgar. Misali, kuɗaɗen zinare sun fi gishiri, fata da makamai sauƙin ɗauka a yi zirga-zirga da su, yayin da su kuma kuɗaɗen takarda sun fi na zinare sauƙin ɗauka da zagayawa duk inda a ke so, kuɗaɗen digital na lambobi kuma sun fi kuɗaɗen takarda sauƙin ɗauka domin a cikin wayarka sai ka ɗauki adadin kuɗaɗen da sai an cika babbar mota da kuɗaɗen takarda ba a iya ɗauke su ba.
4. Non-counterfeitable: Kafin kuɗi ya zama mai nagarta sai idan yana da wahalar kwaikwaya ta yadda mutane ba za su iya yin jabun su ba, saboda idan ya kasance kuɗaɗe suna da sauƙin bugawa to zai zama ba su da daraja ta yadda mutane da yawa za su zaɓi su buga kuɗin maimakon sarrafa kayan da za su sayar su samu kuɗin. A wannan ma idan mu ka duba za mu ga; gishiri, fata, tagulla, tasa da zinare dukkanin su suna da wahalar kwaikwaya ko ma ba za a iya kwaikwayon su ba. Su ma kuɗaɗen takarda suna da wahalar kwaikwaya sakamakon Gwamnati ta keɓe nau'in takarda da tawadar zana su ta yadda za su yi wahalar mallaka ballantana a buga kuɗi da su, duk da a kan samu lokuta da yawa wasu su iya buga jabunsu kuma ya zamanto mutane suna kashe su ba tare da sun iya bambanta jabun da na ainihi ba. Su ma kuɗaɗen digital a nasu ɓangaren suna da wahalar kwaikwaya sakamakon ikon samar da su yana hannun Gwamnati ne ita kaɗai.
5. Valuable: Masana s**a ƙara da cewa, kuɗaɗe ba sa zama cikakkun ingantattu idan
ba su zama suna da daraja a karan-kansu ba. Duk abin da da za a yi amfani da shi a matsayin kuɗi ya dace ya zamto yana da ƙima ta yadda ko da an daina amfani da shi masu shi ba za su yi asara ba, domin za su iya amfani da shi su sarrafa kayan biyan buƙata da za su iya sayarwa a ba su kalar kuɗin da aka koma ana amfani da su. Amma idan ya kasance kuɗaɗe ba su da wata daraja a karan kansu ta yadda idan aka daina amfani da su mai su ba zai iya sarrafa su ba sai dai ya watsar to ba su gama cika masu inganci ba. A wannan fannin ma idan muka duba za mu ga yawancin abubuwan da aka yi amfani da su a matsayin kuɗi suna da amfani don ko da ma ba a ba su matsayin kuɗi ba mutune na amfani da su kamar; gishiri, ƙarafuna, makamai, fata da zinare. Amma kuɗaɗen takarda da kuɗaɗen digital
dukkanin su ba su da wata daraja ko amfani, idan aka daina amfani da su ita kanta Gwamnati ƙona su ta ke yi saboda rashin amfanin su. Darajar kuɗaɗen takarda da na digital daraja ce ta doka, Gwamnati ta zartar cewa a dinga karɓar su saboda haka mutane su ke karɓar su ba don suna da wata daraja ba. Sai dai wasu daga cikin masana kuma suna ganin duk da kuɗaɗen Gwamnati ba su da wani amfani ko daraja a karan kansu, amma wahalar kwaikwaya da su ke da su shi ma daraja ne, don idan ya kasance ba za ka iya samar da abu ba kuma kana buƙatarsa, idan kana son mallakarsa sai ka yi aiki tuƙuru kafin ka samu, to iya wannan ma daraja ne. Koma dai ya ya, suna da darajar ne saboda Gwamnati ta zartar da dokar a ke ƙarbar su, idan gobe ta ce a daina amfani da su to sun zama abin da Hausawa ke kira da "Fasassar ƙota ba ta moriya sai jifa."
6. Generally Acceptability: Abu na ƙarshe kuma mai mahimmanci da ya kamata kowanne kuɗi ya zama yana da shi, shi ne ya zama ilahirin al'umma suna karɓar sa a matsayin kuɗi. Amma idan ya kasance kuɗi ba a ko ina za ka je ka ba da su a karɓa ba, to ba su gama zama masu inganci ba. A wannan fannin ma idan muka duba za mu ga abubuwa da yawa da aka yi amfani da su a matsayin kuɗi a zamaninsu ana karɓar su a kusan ko a ina, kamar zinare da a zamanin da a ke amfani da shi a matsayin kuɗi babu yankin da za ka je ka ba da shi ba a karɓa ba, saɓanin kuɗaɗen Gwamnati wanda a ke karɓa a iya ƙasar da a ke sarrafa su kaɗai. Duk da ya ke kamar Naira duk inda ka je a faɗin Nijeriya ka miƙa ta za a karɓa a ba ka abin da ka ke buƙata, amma a wasu ƙasashen ba za a karɓa ba. Dalilin da ya sa a ke iya karɓar zinare a ko ina cikin faɗin duniya a zamanin da a ke amfani da shi a matsayin kuɗi shi ne, saboda al'umma ne s**a haɗu wajen yarda da shi a matsayin kuɗinsu ba ƙaƙaba masu shi aka yi ba, sannan kowa na iya haƙo shi gwargwadon adadin da zai iya, ba kamar kuɗin Gwamnati da ita kaɗai ce ke da ikon samarwa ba.
Wannan shine karshen darasin mu akan kuɗi. Allah yasa mudace. Ameeeeen ya Allah
Ina tare da Financial Analyst Avokina Comrafe Mubarak Badamasi Babangida
https://www.facebook.com/profile.php?id=100086001708799