08/02/2024
YANDA ZAKA DAWODA LAMBOBIN LAYINKA DA YAFADI
Zaka iya dawo da Lambobin wayarka (Contacts) a lokacin da ka rasa Layin wayar ko wayar, ta amfani da Facebook Account ɗinka zaka dawo dasu..
Ina nufin kamar idan ka rasa Lambobin wayarka masu muhimmanci tunda gaskiya wasu numbers ɗin idan har waya ta ɓace ko layi ƙila an rasasu kenan har'abada, musamman idan baka saving Numbers a Google Drive ko Gmail, ko kuma shima Email ɗin anyi hac-king nasa to amma ta amfani da Facebook Account ɗinka zaka iya dawo da abinka.
Facebook yana reading abubuwa da dama namu, musamman wayoyinmu bama Facebook ba yawancin social media ɗin nan sai kana taka tsantsan sosai ba kaɗan ba.
Akwai yadda zakayi Importing na Contacts ɗinka daga wayarka zuwa Facebook Account ɗinka, ta yadda da zaran ka rasa layinka ko Wayarka kana mallakar wata wayar zaka iya Exporting ɗinsu daga Facebook zuwa wayarka cikin sauƙi, yadda abun yake shine zaka shiga Setting na Facebook ɗinka sai kaje wurin da aka rubuta "Contact Uploading" bayan ya buɗe akwai wani madanni sai ka danna shi, daganan zasu ƙara neman izini a wurinka idan ka danna "ON" shikenan zasu kwaso lambobin wayarka su ajiye a Account ɗinka na Facebook tareda gano maka Abokananka da suke Facebook da lambobin wayar naka.
Note: Ina mai bada shawara idan kasan Account ɗinka bakada tabbas akansa, ma'ana baka cikin masu sanya Strong Password, to karkayi Importing Numbers naka kabarsu kawai, saboda kar azo ka gama kwashe lambobi ka ɗora a Facebook Account naka wani yazo ya ƙwace Account ɗin ya samu Lambobin mutane, amma idan kanada tabbaci akan ingancin tsaron Account ɗinka to kana iya yi.
Allah yataimaka..🙏