22/06/2024
Oga Badamasi Aliyu Abdullahi yace:-
Hanyoyin Da Za Ka Taimaki Mutane Ba Tare Da Ka Kashe Ko Kwabo Ba 👇
1. Sanar da mutane abinda ka sani. Duk wanda ka sanar da shi wani ilimi da bai sani ba kuma wanda zai yi masa amfani, ka taimaki rayuwarsa. Abin sha'awa shi ne a kafar sada zumunta kawai za ka iya ilimantar da dubban ɗaruruwan mutane, ka samu lada. Shi ilmi ko a rubutu saɗara ɗaya za ka iya isar da shi.
2. Aikin Sa Kai. Aikin da ba biyan ka za ayi ba amma wanda zai ciyar da al'umma gaba. Irin tarin waɗannan ayyukan na sa kai (volunteering), na daga cikin abubuwan da ƙasashen da su ka cigaba su ka mayar da hankali wanda mu ke gani mu ke sha'awar su.
3. Sada mutum da wanda zai taimake shi. Idan Allah ya ma ka baiwar sanin mutane, akwai waɗanda taimakon da su ke buƙata bai wuce a yi mu su iso da wani ba. Ma sha ba da misali da Dr. Bala Muhammad wanda ya sha haɗa mu da manyan mutane irin su marigayi Alhaji Bashir Tofa da makamantansu waɗanda in ba don shi ba babu yadda za mu iya samun access da su.
4. Sauraron mutane da ƙarfafa mu su gwiwa. A irin wannan yanayi na ɗimuwa, akwai mutane da yawa ba kuɗin ka su ke buƙata ba. Ba su da wanda zai saurare su ne. Saɓanin yadda wasu ke ɗauka, akwai mutane da yawa da matsalar da ke damunsu ba ta kuɗi ba ce. Da yawa kuma rashin wanda zai saursresu ko ya ƙarfsfesu shi ke jefa su cikin depression.
5. Yaɗa alkhairi. Idan ka ga post mai amfani, yaɗa shi zai amfanar da mutane da yawa ( when everybody shares, everybody enjoys). Idan ka san wani wanda ya ke sana'a, sharing ɗin tallansa ko ambatonsa a social media kawai zai iya zama silar yin ciniki a gare shi. Idan ka ga wani opportunity na tallafi ko na ɗaukar aiki ko na tallafin karatu, yaɗa shi taimakon mutane ne ba tare da ka kashe ko kwabo ba.
6. Participating a community project. Kowa ya na son cigaba amma kowa so ya ke wani, ba shi ba, ya zama silar samun cigaban. Idan kowa zai zauna ya na jiran sai wani ne ko wasu kawai zai kawo masa cigi, to haka za mu yi ta zama babu cigaba. A duk inda ka ke, za ka iya shirya community project, ka nemi wasu ku haɗa ƙarfi da ƙarfe ku yi. In kuma wasu ne, su ka shirya, su ka gayyace ka, sai ka je don bayar da gudunmawarka ga cigaban al'umma.