25/03/2026
⚠️ KIRA, GARGAƊI DA TUNATARWA GA ‘YAN UWA MUSULMI YAN MEDIA DANGANE DA DORA HUTUNAN MUTANE BAYAN SUN MUTU MUSAMMAN MATA⚠️
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Ya ku ‘yan uwa, ya zama dole mu tsaya mu gyara wani abu da ya yawaita a yau, Wannan abu shine ɗora hotunan mamata musamman mata marasa hijabi a social media.
Ku ji abin da Shari’a ta ce:
Allah (SWT) Ya ce:
“Kada su bayyana adon su sai abin da ya bayyana daga gare shi…”
(Suratun Nur: 31)
Wannan yana nuna wajabcin rufe jiki da tsare mutunci, don haka bai halatta a fallasa hoton mace marar hijabi ba – ko tana raye ko ta mutu.
📖 Haka kuma Allah Ya ce:
“Kada ku cutar da muminai maza da mata ba tare da wani laifi ba…”
(Suratul Ahzab: 58)
Yada hoton mamaci da zai jawo fitina ko zubar da mutunci yana cikin cutarwa.
Annabi (SAW) ya ce:
“Kada ku zagi mamata, domin sun riga sun kai ga abin da s**a aikata.”
(Bukhari)
Wannan yana nuna wajibcin girmama mamaci da kiyaye mutuncinsa bayan mutuwarsa kar ka zage shi kar kayi abinda zai sa a zageshi
Kuma ya ce: SAW
“Ku nisanci kururuwa irin na jahiliyya.”
Wato: yada mutuwa da abubuwan da s**a haɗa da kuka, hotuna, ko abubuwan da basu dace ba.
Don haka:
Haram ne a ɗora hoton mace marar hijabi bayan mutuwarta
Bai dace ba a yada hotuna ko bidiyo na mamaci
Haram ne a yi abubuwan da zasu jawo fitina ko kallon haram
✅ Abubuwan da ya HALATTA mu yi:
Sanar da mutuwa cikin natsuwa domin a yi jana’iza
Dalili:
Annabi (SAW) ya sanar da mutuwar Najashi ga sahabbai
(Bukhari da Muslim)
Yin addu’a da neman gafara gare su
Annabi (SAW) ya ce:
“Idan mutum ya mutu, aikinsa ya yanke sai uku…”
(Muslim)
Yin sadaka a madadinsu
Tunatar da mutane su yi musu addu’a
🤲 Ya ku ‘yan uwa:
Mamaci yanzu yana buƙatar addu’a, sadaka da gafara, ba hotuna ba.
Allah Ya shiryar da mu, Ya gafarta wa mamatanmu baki ɗaya. Ameen.
Da fatan za mu gyara wannan kuskure da mukeyia.
Dan uwanku
Hafis Ibrahim Dambam
6/10/1447 - 25/3/2026