09/07/2026
TA YAYA AKE YIN FOREX KAFIN INTERNET?
"Yanzu ga wata tambayar da bantaba gani wani yayi ba."
"Ta yaya ake yin Forex lokacin da babu internet?"
"Masamman saboda idan ka ga yadda ake yin ta a yau..."
"Ka buÉ—e MetaTrader..."
"Ka danna Buy..."
"Nan take order ya shiga."
"Sai ka yi tunanin haka ake yi tun da farko."
"A'a."
Abin ya sha bamban sosai.
Da farko, manyan bankuna ne kawai ke yin wannan musayar kuÉ—i.
Idan wata gwamnati tana son canja kuɗinta zuwa na wata ƙasa, tana amfani da babban bankinta.
Idan wani babban kamfani yana son biyan kuɗin kaya daga wata ƙasa, sai ya je bankinsa.
Bankin kuma zai tuntuɓi wani banki a wata ƙasa.
Ana yin tattaunawa ta sakonni, rubutun takardu da waya dan tabbatar da farashi.
Sannan daga baya a kammala cinikin.
Wani lokaci ma ciniki guda yana iya É—aukar kwanaki kafin a gama.
Ka ga bambancin su da yau?
Yanzu cikin daƙiƙa guda za ka iya siyan Dollar ko ka sayar da Euro.
Amma a wancan lokaci, komai yana tafiya a hankali.
Send a message to learn more